IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Hardar Kur'ani A Afirka Ta Kudu

14:54 - June 18, 2009
Lambar Labari: 1792097
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da gasar kur'ani ta shekara shekara a kasar Afirka ta kudu a birnin Kevtown, da nufin karfafa gwiwar musulmi mazauna kasar wajen mayar da hankali kan karatun kur'ani da hardarsa, da kuma yin aiki da koyarwarsa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani da harkokin musulmin kasar afirka ta kudu cewa; Za a gudanar da gasar kur'ani ta shekara shekara a kasar Afirka ta kudu a birnin Kevtown, da nufin karfafa gwiwar musulmi mazauna kasar wajen mayar da hankali kan karatun kur'ani da hardarsa, da kuma yin aiki da koyarwarsa. Bayanin ya ci gaba da cewa za a kasa bangarorin da za a gudanar da hardar zuwa bangarori daban-daban, da hakan ya hada da hardar kur'ani daga juzu'i na farko zuwa na biyar, hakan nan kuma na goma zuwa na sha biyar da kuam rabin kur'ani, sannan kuma akwai gasa ta dukkanin kur'ani tun daga farko har zuwa karshe.

421571



captcha