Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani taro a kasar Senegal da zai bahasi kan hakkokin yara a cikin kur'ani mai tsarki, a daidai lokacin da ake gudanar da taruka kan ranar kananan yara na nahiyar Afirka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran APS cewa; Za a gudanar da wani taro a kasar Senegal da zai bahasi kan hakkokin yara a cikin kur'ani mai tsarki, a daidai lokacin da ake gudanar da taruka kan ranar kananan yara na nahiyar Afirka. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar wasu daga cikin manyan malaman addinin musulunci na kasar Senegal, da kuma masana daga bangarori daban-daban na kasar da suka hada da malaman jami'a. Ba'ada bayan haka kuma taron zai samu halartar wakilai daga bangarori daban-daban na duniya da kuma wakilai na kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa.
421617