Bangaren kasa da kasa; Gwamnatin kasar Jordan ta bukaci da a kafa gwamnatin hadin kan kasa a kasar Jordan, domin a cewarta hakan ne kawai zai kawo karshen zaman doya da man ja da ake yi tsakanin yahudawan sahyuniya da palastina masu gwagwarmayar kwato 'yancinsu daga mamayar yankunansu da Isra'ila ke ci gaba da yi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana na kasar Syria cewa; Gwamnatin kasar Jordan ta bukaci da a kafa gwamnatin hadin kan kasa a kasar Jordan, domin a cewarta hakan ne kawai zai kawo karshen zaman doya da man ja da ake yi tsakanin yahudawan sahyuniya da palastina masu gwagwarmayar kwato 'yancinsu daga mamayar yankunansu da Isra'ila ke ci gaba da yi. Bayanin ya ci gaba da cewa dole ne Isra'ila ta mutunta dokokin kasa da kasa matukar dai tana son zaman lafiya tsakaninta da palastinawa da ma sauran al'ummomi a yankin gabas ta tsakiya, kuma ta kawo karshen mamaye yankunan palastinawa da ta ke ci gaba da yi a halin yanzu musamman ma a yankunan gabacin Qods da kuma gabar yamma da kogin Jordan.
421628