IQNA

Adadin Musulmi Na Ci Gaba Da Karuwa A Jamhuriyar Chek

Bangaren kasa da kasa; Tun bayan da daular kwaminisanci ta fadi a kasar Solvakia a cikin shekaru ashirin da suka gabata, adadin musulmi da cibiyoyin musulumi da ke gudanar da harkokin yada addinin musulunci na ci gaba da karuwa a kasar da kuma sauran kasashen gabacin nahiyar turai.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; Tun bayan da daular kwaminisanci ta fadi a kasar Solvakia a cikin shekaru ashirin da suka gabata, adadin musulmi da cibiyoyin musulumi da ke gudanar da harkokin yada addinin musulunci na ci gaba da karuwa a kasar da kuma sauran kasashen gabacin nahiyar turai. Bayanin ya ci gaba da cewa daya daga cikin jagororin musulmi a yankin Balkan ya bayyana cewa, addinin musulunci na gaba da yaduwa cikin sauri a yankin, musamman ma a kasashen da suka fuskanci danniya da zalunci daga daulolin guguzu da aka yi a yankin, daga ciki kuwa hard a kasar Chek, wadda cibiyoyin addinin msulunci ke ta karuwa a cikinta a cikin 'yan lokutanan.


421651