Bangaren kasa da kasa: hadin guiwar kungiyoyin addinin musulunci a Lahistan sun fara tattaunawa da gwamnatin wannan kasa domin isa ga Hakkokinsu.
Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga Star ta watsa rahoton cewa: karkashin dokokin wannan kasa na 1936 dole musulman kasar a sallolinsu a massallatai da na juma'a sun rika yiwa shugaban wannan kasa addun'a alhali wannan doka ta sabawa dokoki da ka'ida ta musulunci saboda haka hadin guiwar kungiyoyin musulmi ke tattaunawa da gwamnatin domin ganin an soke wannan doka da kuma ganin ranekun idi na musulmi su zama ranekun hutu a hukumce a wannan kasa.
422274