IQNA

An Gudanar Da Zama Na Musamman Dangane Da Gasar Kur'ani A Moscow

15:33 - June 20, 2009
Lambar Labari: 1792692
Bangare kasa da kasa; An gudanar da wani zama na musamman dangane da gasar kur'ani mai tsarki da za a gudanar a birnin Moscow na kasar Rasha.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ruvur.ir cewa; shugaban kwamitin kula da harkokin addini na kasar Rasha Roshan Abbas ya bayyana cewa; An gudanar da wani zama na musamman dangane da gasar kur'ani mai tsarki da za a gudanar a birnin Moscow na kasar Rasha.Ya ci gaba da cewa wannan gasa a matsayin gasa ta kasa da kasa take, domin kuwa sama da kasashe 30 ne za su halarci gasar, ya ce wannan shi ne karon farko da za a gudanar da wata gasar kur'ani mai tsarki da za ta kashen duniya kamar haka a birnin Moscow fadar mulkin kasar Rahsa, kuma za a fara gudanar da gasar ne a cikin watan Yuli mai kamawa, inda makaranta da mahardata kur'ani daga kasashen musulmi daban-daban za su halarci gasar, daga ciki kuwa hard a kasar Saudiyya.

422224
captcha