Bangaren kasa da kasa; Kwamitin hadin gwiwa da ke kula da gudanar da ayyukan musulunci a duniya zai gudanar da zamansa a karo na goma sha shida a birnin Tripoli na kasar Libya, tare da hadin gwiwa da kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na kungiyar gadin kan kasashen musulmi ta OIC cewa; Kwamitin hadin gwiwa da ke kula da gudanar da ayyukan musulunci a duniya zai gudanar da zamansa a karo na goma sha shida a birnin Tripoli na kasar Libya, tare da hadin gwiwa da kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC. Kwamitin wanda ya hada kungiyoyi da cibiyoyin addinin musulmunci sama da 40 daga sassa daban-daban na kasashen duniya, zai yi dubi ne a zaman nasa na birnin Tripoli kan muhimman batutuwa da suke ci ma al'ummar musulmi tuwo a kwarya a cikin wannan zamani, da hakan ya hada da cin zarafin da ake yi wa musulmi da mabiya addinin musulunci a wasu kasashe na yammacin turai, tare da daukar matakan da suka dace da nufin kawo karshen hakan.
422206