Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar saudiyya was cewa; An kawo karshen zaman da kungiyoyin hardar kur'ani suka gudanar na bayar da horo ga matasa masu sha'awar hardar kur'ani mai tsarki a lardin kura a kasar Saudiyya. Bayanin ya ci gaba da cewa hukumar kula da ayyukan taimakon musulunci ta kasar saudiyya ita ce ta dauki nauyin gudanar da wannan zaman bayar da horo na hardar kur'ani ga matasa na kasar Saudiyya. Wannan dai shi ne karo na uku da hukumar ke daukar nauyin gudanar da irin wannan shiri na bayar da horo na hardar kur'ani mai tsarki a kasar. A wannan karon shirin ya samu karbuwa daga matasa fiye da shekarun baya.
422223