IQNA

An Gudanar Da Taro Kan Mu'ujizar Kur'ani A Kasar Turkiya

15:32 - June 20, 2009
Lambar Labari: 1792695
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani taro kan mu'ujizar kur'ani da aka bai wa taken kur'ani babbar mu'ujiza, wanda kwamitin da ke kula da harkokin addini na kasar Turkiya ya shirya gudanarwa a birnin Manisa na kasar turkiya.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran manisalife cewa; sakataren kwamitin kula da harkokin kur'ani na kasar Turkiya Khalid Abu Najul ya bayyana cewa; An gudanar da wani taro kan mu'ujizar kur'ani da aka bai wa taken kur'ani babbar mu'ujiza, wanda kwamitin da ke kula da harkokin addini na kasar Turkiya ya shirya gudanarwa a birnin Manisa na kasar turkiya. Ya ci gaba da cewa wannan taron ya yi tasiri matuka wajen wayar da kan da dama daga cikin al'ummomin yankin wadanda suke da shawar sanin kur'ni mai tsarki da ilmomin da ke cikinsa. Ya ci gaba da cewa da dama daga cikin malamai dam asana da suka halarcin zaman taron da suka gabatar da jawabai da laccoci sun mayar da hankali ne wajen nuna matsayin kur'ani mai tsarki da kuma hikimomin da ke cikinsa, wadanda dukkanin shirya na nan tattare da su matukar dai dan adam ya sa hankali da lura a cikin wajen fahimtar hakikanin ma'anarsu.

421864
captcha