IQNA

ISESSCO Za Ta Gudanar Da Taro Hanyoyin Koyar Da Ilimin Addinin Musulunci

Bangaren kasa da kasa; Kungiyar kula da harkokin ilimi da aladun addinin musulunci ta ISESSCO za ta gudanar da wani zaman taro da zai dubi dangane da hanyoyin da ya kamata a yi amfani da su wajenn koyar da ilmomin addinin musulunci a makarantu da ke cikin kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren hulda jama'a na na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC cewa; Kungiyar kula da harkokin ilimi da aladun addinin musulunci ta ISESSCO za ta gudanar da wani zaman taro da zai dubi dangane da hanyoyin da ya kamata a yi amfani da su wajenn koyar da ilmomin addinin musulunci a makarantu da ke cikin kasashen musulmi. Sakataren kungiyar ya bayyana cewa kafa wata gamayyar manyan kungiyoyi na duniya domin samun sulhu da zaman lafiya a fadin duniya. Tuwaijari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi dangane da kaddamar da wani littafi da aka yi kan ci gaban al'du da addinai a duniya. Ya ce kafa wannan gamayya zai taimaka wajen hada kan al'ummomin duniya da suke da mabanbantan addinai da al'adu, tare da samun sulhu da fahimtar juna da kuma girmama al'adu da akidu gami da addinin kowane bangare daga cikinsu. Haka nan kuma wannan gamayya za ta iya yin aiki tare da majalisar dinkin duniya kai tsaye.
422223


422199