IQNA

ISESCO Ta Bukaci Da A Kafa Kawancen Manyan Kungiyoyi Domin Samun Sulhu

Bangaren kasa da kasa; Babban sakataren kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adun musulunci Abdulaziz Usman Al-tuwaijari ya bukaci da a kafa wata gamayyar manyan kungiyoyi na duniya domin samun sulhu da zaman lafiya a fadin duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labarai na MAP cewa; Babban sakataren kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adun musulunci Abdulaziz Usman Al-tuwaijari ya bukaci da a kafa wata gamayyar manyan kungiyoyi na duniya domin samun sulhu da zaman lafiya a fadin duniya. Tuwaijari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi dangane da kaddamar da wani littafi da aka yi kan ci gaban al'du da addinai a duniya. Ya ce kafa wannan gamayya zai taimaka wajen hada kan al'ummomin duniya da suke da mabanbantan addinai da al'adu, tare da samun sulhu da fahimtar juna da kuma girmama al'adu da akidu gami da addinin kowane bangare daga cikinsu. Haka nan kuma wannan gamayya za ta iya yin aiki tare da majalisar dinkin duniya kai tsaye.


422224