IQNA

Za A Gudanar Da Taro Na Kasa Da Kasa Kan Musulunci A Nahiyar Turai

16:36 - June 21, 2009
Lambar Labari: 1793154
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar ta taro na kasa da kasa a karo na biyu mai taken musulunci a nahiyar turaia birnin Kazabalnka na kasar Morocco.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar shark alausat cewa; Za a gudanar ta taro na kasa da kasa a karo na biyu mai taken musulunci a nahiyar turaia birnin Kazabalnka na kasar Morocco. Shugaban kwamitin kula da harkokin musulmi marassa rinjaye a nahiyar turai Abdullah Bu Suf ya bayyana cewa; babbar manufar gudanar da taron ita ce karfafa gwiwar musulmi da suke zaune a nahiyar turai wajen ci gaba da gudanar da ayyukansu da harkokinsu na addini, da kuma sanin hanyoyin da za a bi wajen karfafa kungiyoyin musulmin, da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama da ke fafutukar kare hakkokin musulmi wadanda su ne marassa rinjaye a cikin kasashen turai.


422554



captcha