Bangaren kasa da kasa; kafofin yada labarai na kasashen waje, musamman ma na kasashen larabawa da na kasashen yammacin turai, sun watsa hudubar juma'a da jagoran juyin juy ahalin musulunci na Iran Ayatollah khamenei ya gabatar kai tsaye, dangane da batutuwan zabe da kuma abubuwan da suka biyo bayan sanar da sakamakon zaben.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alarab yaum cewa; kafofin yada labarai na kasashen waje, musamman ma na kasashen larabawa da na kasashen yammacin turai, sun watsa hudubar juma'a da jagoran juyin juy ahalin musulunci na Iran Ayatollah khamenei ya gabatar kai tsaye, dangane da batutuwan zabe da kuma abubuwan da suka biyo bayan sanar da sakamakon zaben. Rahoton ya ci gaba da cewa, wadannan kafofin yada labarai sun dauki hudubar ne kai tsaye saboda matukar muhimmancin da take da shi. Wasu daga cikin kafofin yada labaran sun yi ta yin amfani da hudubar domin kara gishiri da zuzuta abin da yake faruwa a cikin gida a Iran a halin yanzu, inda suke bayyana hakan a matsayin wani juyin juya hali sabo.
422567