IQNA

Za A Gudanar Da Wani Taron Raya Harkokin Musulunci A Afirka

16:35 - June 21, 2009
Lambar Labari: 1793156
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani taron raya harkokin addinin musulunci a Afirka, wanda za a gudanar a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran APS cewa; Za a gudanar da wani taron raya harkokin addinin musulunci a Afirka, wanda za a gudanar a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wannan taro ita ce kara bayyana hanyoyin da ya kamata musulmi su bi domin yada addinin msulunci a nahiyar afirka. Daga cikin irin wadannan muhimman hanyoyi kuwa har da kafa cibiyoyi na ilimi domin yada ilmin addinin musulunci ga sauran al'ummomi da bas u da masaniya kansa, gami da gina wuraren ibada, da kuma cibiyoyi na fadakarwa.

422605








captcha