IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Matsayin Al'adu A Addinin Musulunci

16:35 - June 21, 2009
Lambar Labari: 1793158
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da taro na kasa da kasa dangane da matsayin al'adu a mahangar addinin musulunci, wanda za a gudanar a kasar Spain a birnin Kordoba da ke kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na islam cewa; Za a gudanar da taro na kasa da kasa dangane da matsayin al'adu a mahangar addinin musulunci, wanda za a gudanar a kasar Spain a birnin Kordoba da ke kudancin kasar. Taron zai mayar da hankali ne kan mahangar addinin musulunci dangane da al'adun al'ummomi. Sakataren OIC y ace al'adu suna da matsayi na musamman aaddinin musulunci, Tuwaijari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi dangane da kaddamar da wani littafi da aka yi kan ci gaban al'du da addinai a duniya. Ya ce kafa wannan gamayya zai taimaka wajen hada kan al'ummomin duniya da suke da mabanbantan addinai da al'adu, tare da samun sulhu da fahimtar juna da kuma girmama al'adu da akidu gami da addinin kowane bangare daga cikinsu. Haka nan kuma wannan gamayya za ta iya yin aiki tare da majalisar dinkin duniya kai tsaye.



422491
captcha