IQNA

Za A Gudanar Da Taron Yaye Dalibai A Jami'ar Musulunci Ta Turkiya

16:35 - June 21, 2009
Lambar Labari: 1793160
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da taron yaye dalibai da suka kammala karatu a bangaren tauhidi a kwalejin ilimin ilihiyat da ke kasar Turkiya, wanda cibiyar kula da harkokin dalibai da ke karatun tauhidi ta shirya ga dukkanin dalibai da suka kammala karatunsu a wannan reshe.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran tidamider na kasar Turkiya cewa; Za a gudanar da taron yaye dalibai da suka kammala karatu a bangaren tauhidi a kwalejin ilimin ilihiyat da ke kasar Turkiya, wanda cibiyar kula da harkokin dalibai da ke karatun tauhidi ta shirya ga dukkanin dalibai da suka kammala karatunsu a wannan reshe. Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai dalibai da suka kammala karatunsu a bangaren ilahiyat daga wasu sassa na jami'oin kasar wadanda duk za su halarci taron domin samun wannan sheda ta musamman. Daga cikin wadanda za su halarci taron akwai jami'an gwamnati da kuma malaman addinin muslunci na kasar.


422495


captcha