IQNA

An Fara Gudanar Da Baje Koli Dangane Da Yaduwar Musulunci A Latin Amurka

16:35 - June 21, 2009
Lambar Labari: 1793161
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani baje kolin kayyaki da ke nuni da yadda musulunci ya fara shiga yankunan latin Amurka, da kuma tasirin da yake da shi a tsakanin al'ummar yankin, wanda ma'aikatar harkokin kula da al'adu ta kasar morocco ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin Rebat
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar alwatan cewa; An fara gudanar da wani baje kolin kayyaki da ke nuni da yadda musulunci ya fara shiga yankunan latin Amurka, da kuma tasirin da yake da shi a tsakanin al'ummar yankin, wanda ma'aikatar harkokin kula da al'adu ta kasar morocco ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin Rebat. Daga cikin abubuwan da ake nunawa awurin baje kolin hard a zane-zane da ke nuna irin tasirin da musulunci yake a tsakanin al'ummomin yankin, da kuma yadda suke nuna sha'awarsu dangane da koyarwa irin ta addinin musulunci da yadda yake shiryar dad an adam tare da koyar da shi kyawawan dabi'u, wadanda sun e dabi'u da suka dace da shi da fitirarsa.

422460



captcha