Bangaren harkokin kur'ani: an kaddamar da wani shafin internet a fadin kasar ta Indonosiya da zai fi maida hanakali da kawo labarai da suka shafi gasar kur'ani da hadisan Manzon Allah (SWA) na Sultan bin Abdul aziz.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton daga kudu maso gabacin Asiya baya ta nakalto daga majiyar labarai ta Saudiya Was cewa wannan shafin Internet na kur'ani an kaddamar da shi ne tare da hadin guiwar ma'aikatar kula da harkokin addini na Indonosiya kuma a lokacin kaddamar da bukin da wannan shafi an samu halartar Abdulrahman Muhammad Amin AlKhayat jakadan kasar Saudiya a Indonosiya da kuma wasu wakilan gwamnatin Saudiya da Indonosiya.
422539