Bangaren ilimi da Nazari;ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Ghana ne ya shirya wannan taro day a hada musulmi da kiristoci.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; Malama Ilzabet da Fatima Suleiman mambobi a komitin ilimi na jami'ar Lgon da shugabanni na muassisoshi da cibiyoyi na ilimi gami da wakilan ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a ketare suna daga cikin wadanda suka halarci wannan taro da kuma gabatar da jawabai masu gamsarwa kan yadda addinin musulunci da na kirista suke tasiri da taka rawar gani a rayuwar iyali da zamantakewa.
422420