IQNA

Za A Fitar Da Bayanai Kan Tattaunawa Tsakanin Musulmi Da Kirista A Birtaniya

15:48 - June 22, 2009
Lambar Labari: 1793239
Bangaren kasa da kasa; A karon farko za a fitar da wani littafi da ya danganci tattaunawa tsakanin mabiya addinin musulunci da kuma mabiya addinin kirista a kasar Birtaniya, dangane da yadda ya kamata bangarorin biyu su fahimci junansu, domin samun fahimta juna da zaman lafiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Christian Today cewa; A karon farko za a fitar da wani littafi da ya danganci tattaunawa tsakanin mabiya addinin musulunci da kuma mabiya addinin kirista a kasar Birtaniya, dangane da yadda ya kamata bangarorin biyu su fahimci junansu, domin samun fahimta juna da zaman lafiya. Bayanin ya ci gaba da cewa kungiyoyin mabiya addinin musulunci da kuma mabiya addinin kirista ne suka shirya gudanar da tattaunawar da nufin kusanto da fahimta a tsakaninsu, kuma hakan zai bayar da dama wajen kara shimfida hanyar samun sulhu da kawar da kyamar juna. Bayanin ya ci gaba da cewa hakan zai bayar da damar fadada wannan irin wannan dganta da sauran addinai.


422689



captcha