Bangaren kasa da kasa; Wata babbar kungiyar yahudawan kasar Canada ta shelanta hadewata da gamayyar kungiyoyin yahudawa da suka haramta samuwar Isra'ila ta BDS, wadda aka kafa a cikin shekara ta 2005, kuma kungiyar ta kirayi gwamnatin kasar Canada da ta shelanta Isra'ila a matsayin haramtacciyar kasa.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran ma'a cewa; Wata babbar kungiyar yahudawan kasar Canada ta shelanta hadewata da gamayyar kungiyoyin yahudawa da suka haramta samuwar Isra'ila ta BDS, wadda aka kafa a cikin shekara ta 2005, kuma kungiyar ta kirayi gwamnatin kasar Canada da ta shelanta Isra'ila a matsayin haramtacciyar kasa. Kungiyar yahudawan ta bayyana dalilanta na hadewa da gamayyar kungiyoyin yahudawa da suka haramta samur Isra'ila da cewa; Isra'ila kasa ce ta aka samara ta hanyar zalunci da danniya da keta hurumin dan adam, kuma take ci gaba da kasancewa ta hanyar shan jinin fararen hula mata da kananan yara, tare da yin fatali da dukkanin dokoki na kasa da kasa, wanda hakan ya sabawa sahihiyar koyarwa ta addinin yahudanci.
422979