Bangaren kasa da kasa; Wasu daga cikin malaman shi'a a kasar Bahrain sun bayyana cewa babu wani canji da aka samu a cikin siyasar gwamnatin Amurka dangane da kasashen musulmi da kuma addinin muulunci, da kuma goyon baya na ido rufe da take baiwa Isra'ila.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Awal cewa; Wasu daga cikin malaman shi'a a kasar Bahrain sun bayyana cewa babu wani canji da aka samu a cikin siyasar gwamnatin Amurka dangane da kasashen musulmi da kuma addinin muulunci, da kuma goyon baya na ido rufe da take baiwa Isra'ila. Daya daga cikin manyan malaman addini kuma daya daga cikin jagororin mabiya mazhabar shi'a a kasar Bahrain Ayatollah isa Ahmad kasim ya bayyana cewa; Shehin malamin ya ci gaba da cewa a lokacin da shugaban amurka ya barrack obama ya gabatar da jawabinsa a birnin Alkahira, ya yi kokarin jawo hankalin al'ummar musulmi tare da samun goyon bayansu, amma kuma a lokaci guda ya tabbatar musu da cewa aikinsa ne ya kare dukkanin manufofin Isra'ila.
423009