Bangaren kasa da kasa; A wani zama na hadin gwiwa tsakanin malaman addinin musulunci na kasar Morocco da kuma malaman addinin musulunci na kasar Tunisia suka gudanar, sun kirayi dukkanin al'ummar musulmi zuwa ga hadin tare da yin watsi da duk wasu banbance-banbancen mazhaba da abin day a yi kama da haka.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin internet na casafree cewa; A wani zama na hadin gwiwa tsakanin malaman addinin musulunci na kasar Morocco da kuma malaman addinin musulunci na kasar Tunisia suka gudanar, sun kirayi dukkanin al'ummar musulmi zuwa ga hadin tare da yin watsi da duk wasu banbance-banbancen mazhaba da abin da ya yi kama da haka. Bayanin ya ci gaba da cewa, mahalarta taron sun bayyana cewa makiya musulunci suna yin aiki dare da rana domin su raba kan al'ummar musulmi, wanda kuma ci gaba da samun rarraba tsakanin msulmi na nufin makiya sun yi nasara kenan. Bayanin ya kara da cewa babbar hanyar kawo karshen makircin makiya ita ce hada kan al'ummar musulmi.
423020