Bangaren kur'ani; An fara gudanar da gasar kur'ni ta kasa da kasa a birnin Moscow na kasar Rasha, wanda kuma wannan shi ne karo na goma da ake gudanar da irin wannan babbar gasar kur'ani a kasar Rasha.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; An fara gudanar da gasar kur'ni ta kasa da kasa a birnin Moscow na kasar Rasha, wanda kuma wannan shi ne karo na goma da ake gudanar da irin wannan babbar gasar kur'ani a kasar Rasha. Rahoton ya ci gaba da cewa mahardata kur'ani daga kasashe daban-daban ne ke halartar wannan gasa, da suka hada da Turkiya, Algeria Yeman Masar, Indonesia, Malazia Filland Iran Rasha da sauransu. Daga cikin alkalan gasar akwai wani dan kasar iran day a shahara wajen gudanar da alkalancin gasar kur'ani a sassa daban-daban na duniya.
423038