Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na ma'aikatar tsaron jamhuriyar musulunci ta Iran cewa; Mutanen Iran da Labanan da kuma palastinu ba za su taba mantawa da irin rawar da shahid Chamran ya taka ba wajen gina gwagwarmayarsu domin tabbatar da gaskiya da adalci da kuma kawo karshen zalunci da danniya. Bayanin ya ci gaba da cewa shahid Chamran mutum ne da ya bayar da lokacinsa domin yi wa addinin musulunci hidima da kuma al'ummar musulmi. Daga cikin muhimman ayyukan da ya gudanar har da kafa kungiyoyin gwagwarmaya a cikin gida da waje domin yaki da zalunci da kuma danniyar yahudawan sahyuniya, wanda al'ummar musulmi ba ta gushe tana ganin amfanin hakan ba, musamman ma a palastinu da Labanan.
423060