Bangaren siyasa da zamantakewa; a birnin Istambul na kasar Turkiya an fara binciken sanin ci gaban da koyarwa ta samu a kasashen musulmi.
Daga Turkiya cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Muhit ta watsa rahoton cewa; Ibtihaj Abdul Kadir Alkamal daya daga cikin manyan jami'ai a ma'aiakatar ilimi a Yaman ya bayyana cewa: a wannan taro na kwanaki uku sun yi bincike da nazari ne kan muhimman abubuwa da suka shafi ilimi da ci gabansa da kuma yadda koyarwa a kasashen musulmi ta samu ci gaba da wanzuwa.
423033