Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; Kwamitin kula da harkokin kur'ani na kasar Amurka ya sanar cewa yana ci gaba da gudanar da ayyukansa na kur'ani a kasar Amurka kamar yadda ya kamata a bangaren harder kur'ani da kuma karatun tajwidi. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar kafa wannan kwamiti ita ce saukaka wa musulmi masu kokarin koyon karatun kur'ani a kasar Amurka, muamman ma masu sha'awar harder kur'ani. An kafa wannan kwamiti ne tun a cikin shekara ta 1990 , inda masana harkokin addinin musulunci daga cikin mabiya addinin musulunci na kasar ke ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaban musulunci musamman ma ta fuskacin kur'ani.
423583