Bangaren kasa da kasa; An bude wata sabuwar cibiyar kula harkokin kur'ani ta hakan ya hada da harda da karatu ta nakasassu a kasar Kuwait, wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ta bude.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alra'ayi ta kasar Kuwait cewa; An bude wata sabuwar cibiyar kula harkokin kur'ani ta hakan ya hada da harda da karatu ta nakasassu a kasar Kuwait, wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ta bude. Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban bangaren kula da harkokin kur'ani na ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Kuwait Muhammad Umar ya bayyana cewa; babbar manufar samara da wannan cibiya ita ce tamaka wa nakasassu ta fuskacin karatun kur'ani da kuma sanin yadda za su karanta kur'anin da kuma hardarsa, ya ci gaba da cewa harkokin da cibiyar za ta kula da su bai takaitu da kur'ani ba, har da hukunce-hukunce na shari'a da sauransu.
423626