IQNA

An Fitar Da Shirye-Shiryen Kur'ani Da Tashar Risalah A Watan Ramadan

16:16 - June 23, 2009
Lambar Labari: 1793993
Bangaren kasa da kasa; Tashar talabijin din Risalah ta kasar saudiyya ta sanar cewa ta fitar da dukkanin shirye-shirye na kur'ani da za ta watsa a cikin watan Ramadan mai zuwa, wanda za ta watsa kai tsaye a kan tauraron dan adam daga dakin watsa shirye-shiryenta.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Syria post cewa; Tashar talabijin din Risalah ta kasar saudiyya ta sanar cewa ta fitar da dukkanin shirye-shirye na kur'ani da za ta watsa a cikin watan Ramadan mai zuwa, wanda za ta watsa kai tsaye a kan tauraron dan adam daga dakin watsa shirye-shiryenta. Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin muhimman abubuwan da tashar za ta mayar da hankali kansu ta fuskacin kur'ani a cikin shirye-shiryenta a watan Ramadan mai zuwa har da yada ma'anonin kur'ani kai tsaye daga littafan tafsiri na magabata, tare da gayyatar manyan malaman musulunci domin karin haske dangane da ma'anar wasu daga cikin ayoyi da za a mayar da hankali kan tafsirinsu a cikin shirye-shiryen. Ba'ada bayan haka kuma akwai shirye-shirye da suka danganci hukunce-huunce na shari'ar musulunci da malamai za su yi bahasi kansu.

423700


captcha