Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da taron maulidin Imam Ali (AS) a kasar Birtaniya, domin tunawa da zagayowar ranar haihuwarsa mai albarka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Birtaniya cewa; Za a gudanar da taron maulidin Imam Ali (AS) a kasar Birtaniya, domin tunawa da zagayowar ranar haihuwarsa mai albarka. Bayanin ya ci gaba da cewa malaman musulmi a kasar Birtaniya za su halarci wannan babban taro mai matukar muhimmanci ga dukkanin al'ummar musulmi, da suka hada da mabiya mahbar shi'a da kuma 'yan sunna, gami da malaman jami'a da kuma wasu masa musulmi. Za a gudanar da taron ne a babban ginin cibiyar kula da ahrkokin addinin musulunci da ke birnin London.
423156