IQNA

An Fara Gudanar Da Taron Jami'oin Kasashen Musulmi

Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da taron gamayyar jami'oin kasashen musulmi a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya, wanda shuagaban jami'ar Azad ta kasar Iran Dr. Abdullah Jasibi ke jagoranta.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya was cewa; An fara gudanar da taron gamayyar jami'oin kasashen musulmi a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya, wanda shuagaban jami'ar Azad ta kasar Iran Dr. Abdullah Jasibi ke jagoranta. Bayanin ya ci gaba da cewa babban dalilin gudanar da taron shi ne ci hada kan jami'oin kasashen musulmi tare da fayyace muhimman ayyukan day a kamta su mayar da hankali kansu. Daga cikin muhimman abubuwan da taron ke yin dubin a kansu har da daukar matakai na mayar da martani a ilmance dangane da yadda wasu masana a jami'oin kasashen turai suke kokarin gurbata manufar addinin musulunci a cikin nahiyar turai, wanda hakan na bukatar masana musulmi musamman ma dai malaman jami'oi su mayar da hankali kansa domin kare addinin musulunci daga zagon kasa.

423483