Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana na kasar Syria cewa; Babban malamin birnin Qods da ke bayar da fatawa ga musulmin birnin Sheikh Muhammad Hussein Ya bayyana cewa wajibi ne da ya rataya kan al'ummar musulmi da kuma al'ummomin larabawa da su kubutar da birbnin Qods da masallaci mai lafarma daga barazar yahudawan sahyuniya. Rahoton ya ci gaba da cewa malamin ya jaddada wajabcin mikewa tsaye domin kubutar da masallacin Qods mai alfarma, kuma hakan ba za ta yuwu ba har sai musulmi da larabawa sun mike sun nuna da gasket suke . A bangare guda ya bayyana cewa dole al'ummomin palastinu su hada kansu su kawo karshen sabanin da ke akwai tsakaninsu, matukar dai suna son su kubukatar da Qods.
423528