IQNA

Za A Fara Gudanar Da Shirin Bayar Da Horon Karatun Kur'ani A Qatar

15:10 - June 23, 2009
Lambar Labari: 1794044
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da wani shiri na horar da mata karatun kur'ani mai tsarki a birnin Doha na kasar Qatar, wanda cibiyar kula da harkokin karatun kur'ani da hardarsa ta kasar Qatar ta shirya gudanarwa har tsawon watanni biyu masu zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alraya ta kasar Qatar cewa; Za a fara gudanar da wani shiri na horar da mata karatun kur'ani mai tsarki a birnin Doha na kasar Qatar, wanda cibiyar kula da harkokin karatun kur'ani da hardarsa ta kasar Qatar ta shirya gudanarwa har tsawon watanni biyu masu zuwa. Bayanin ya ci gaba da cewa Kwamitin wanda ya hada kungiyoyi da cibiyoyin addinin musulmunci sama da 40 daga sassa daban-daban na kasashen duniya, zai yi dubi ne a zaman nasa na birnin Tripoli kan muhimman batutuwa da suke ci ma al'ummar musulmi tuwo a kwarya a cikin wannan zamani, da hakan ya hada da cin zarafin da ake yi wa musulmi da mabiya addinin musulunci a wasu kasashe na yammacin turai, tare da daukar matakan da suka dace da nufin kawo karshen hakan.

423541

captcha