IQNA

Karamin Birnin Mahajjata Za A Kaddamar Da Shi A Tsakiyar Watan Sha'aban

Bangaren kasa da kasa: Amir Fahad bin Sultan bin Abdul Aziz amiri yankin tabuk nna kasar Saudiya ya bada labarin kaddamar da wannan karamin gari da ke gaf da kan iyakar kasar da Jodan.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta kasar Saudiya Nasij ta jiyo amir Fahad bin Sultan bin Abdul Aziz na cewa: a wannan hali da ake ciki akwai karuwar maniyata aikin hajji masu yawa da ke biyowa ta kan iyakar kasar da kasar Jodan. Ya kara da cewa; saboda haka wannan gari zai taimkawa maniyata da ke bi ta wannan hanya don ziyartar dakin Allah damar hutawa da yada zango a kan hanya.

424085