Jami'ar Almustapha (SWA) Al'alami Ta Sa Hannu Kan Yarjejeniya Da Ma'aikatar Haji ta afganistan
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; ta nakalto daga ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a kasar ta Afganistan tana mai tabbatar da sa hannu a kan wata yarjejeniyar fahimtar juna tare da jami'ar Almustapha (SWA) al'alami kuma daga cikin abubuwan da suka cimma matsaya guda akwai maganar yada ilimi da karawa juna ilimi lokaci zuwa lokaci da kuma masanyar kwararru da malumman masallatai da masu bada horo kan aikin hajji da bawa dalibai damar ci gaba da karatu a jami'ar da sauran abubuwa na ci gaban ilimi da zamantakewa.
424061