IQNA

Littafin Hakkokin Dan Adam A Mahangar Musulunci Ya Samu Karbuwa

22:54 - June 24, 2009
Lambar Labari: 1794585
Bangaren kasa da kasa; Littafin nan mai suna hakkokin dan adam a mahangar musulunci wanda malamin shi'a nan na kasar Saudiyya Hassan Saffar ya rubuta, yana daya daga cikin littafan da suka fi samun kasuwa a dukkanin wuraren da ake sayar dalittafai a kasashen musulmi da na turai a cikin shekara ta 2008.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na saffar.org cewa; jaridar nan da ake bugawa a birnin London na kasar Birtaniya Qods alarabi ta watsa wani rahoto da ke cewa; Littafin nan mai suna hakkokin dan adam a mahangar musulunci wanda malamin shi'a nan na kasar Saudiyya Hassan Saffar ya rubuta, yana daya daga cikin littafan da suka fi samun kasuwa a dukkanin wuraren da ake sayar dalittafai a kasashen musulmi da na turai a cikin shekara ta 2008. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin wannan littafi marubucin Hassan saffar ya yi kokarin bayyyana mahangar addinin musulunci dangane da hakkokin dan adam, sabanin yadda wasu da ke kallon kansu masana a kasashen turai ke kokarin bayyanawa.


424291





captcha