IQNA

ISESCO Za Ta Halrci Taron Gwajin Maguguna Ta Hanyar Internet

22:53 - June 24, 2009
Lambar Labari: 1794587
Bangaren kasa da kasa; Kungiyar yada al'adu da ilimin addinin musulunci ta ISESCO za ta halarci taron gwada magunguna ta hanyar internet, wanda za a gudanar a birnin Qirwan na kasar Tunisia tare da hadin gwiwa da ma'ikatar kula harkokin kiwon lafiya ta kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ise cewa; Kungiyar yada al'adu da ilimin addinin musulunci ta ISESCO za ta halarci taron gwada magunguna ta hanyar internet, wanda za a gudanar a birnin Qirwan na kasar Tunisia tare da hadin gwiwa da ma'ikatar kula harkokin kiwon lafiya ta kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa za a gudanar da taron ne domin yin bahasi kan yadda za a rika tarbar cututtuka da ke shigowa cikin kasashen musulmi daga wasu kasashen, tare da bayar da masaniya ga sauran masana na kasashen kan harkokin lafiya hanyoyin da za su bi wajen hana irin cututtuka a cikin kasashen musulmi, da kuma shawo kansu idan har sun kutsa ba tare da an lura ba. Taron zai samu halartar wakilai daga kasashe daban-daban a matsayi na gwamnati da kuma masana kan harkokin kiwon lafiya.


424275

captcha