Bangaren kasa da kasa; A ci gaba da matsa lamba da ake yi kan Harammtacciyar Kasar Isra'ila na ta kawo karshen killace zirin Gaza da ta ke ci gaba da yi, an shirya gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a kusa da mashigar azr da ke yankin kudancin zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Ikna yanakalto daga kamfanin dillancin labaran ma'an cewa; A ci gaba da matsa lamba da ake yi kan Harammtacciyar Kasar Isra'ila na ta kawo karshen killace zirin Gaza da ta ke ci gaba da yi, an shirya gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a kusa da mashigar azr da ke yankin kudancin zirin Gaza. Kwamitin fafutukar neman kawo karshen killace zirin Gaza shi ne ya shirya guudanar da wannan jerin gwano . Daga cikin irin taken da za a rika rerawa wajen gudanar da zanga-zangar akwai neman a kawo karshen zaluncin da Isra'ila take yi kan al'ummar gaza, da kuma palastinawa na birnin Qods da gabar yammada kogin Jordan, tare da barin dukkanin palastinawa da ke waje su koma gida.
424226