IQNA

An Kawo Karshen Taron Kwamitin Kula Da Ayyukan Musulunci

22:52 - June 24, 2009
Lambar Labari: 1794593
Bangaren kasa da kasa; Kwamitin da ke kula da ayyukan addinin musulunci na kasa da kasa da ke karkashin kulawar kungiyar hada kan kasashen musulmi ta OIC ya kawo karshen taronsa wanda ya gudanar a karo na goma sha shida.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; Kwamitin da ke kula da ayyukan addinin musulunci na kasa da kasa da ke karkashin kulawar kungiyar hada kan kasashen musulmi ta OIC ya kawo karshen taronsa wanda ya gudanar a karo na goma sha shida. Bayanin ya ci gaba da cewa taron wanda ya kwashe tsawon kwanaki uku jere ana gudanar da shi, ya yi dubi kan irin rawar da wannan kwamiti ke takawa ta fuskacin yada al'adu da kuma manufofin addinin musulunci musamman ma a kasashen da ba na musulmi, da suka hada da kasashen yammacin turai. Mahalartar taron sun yi dubi dangane da hanyoyin da ya kamata a bi wajen karfafa wannan kwamiti, tare da fadada ayyukansa a ko'ina cikin fadin duniya.

424133


captcha