IQNA

An Wallafa Wani Kamus Din Kalmomi Da Suka Danganci Musulunci

22:51 - June 24, 2009
Lambar Labari: 1794595
Bangaren kasa da kasa; An wallafa wani kamus din kalmomi da suka danganci addinin musulunci da yaren Spain, wanda kuma wannan shi ne karon farko da aka wallafa irin wannan kamus din.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Garsia cewa; An wallafa wani kamus din kalmomi da suka danganci addinin musulunci da yaren Spain, wanda kuma wannan shi ne karon farko da aka wallafa irin wannan kamus din. Bayanin ya ci gaba da cewa fitaccen malamamin adabin larabcin na jami'ar Barcalona shi ne ya rubuta kamus din, bayan day a kwashe kimanin shekaru goma yana ta kokarin hada kalmomi da za su taimaka ma masu nazari kan ala'du da tarihin musulunci. Daga cikin abin da kamus din ya kunsa akwai kalmomi da ake amfani da su a fikihun musulunci, da kuma banbancin mazhabobin musulunci, da yadda wasu kalmomi suka kebantu da wasu mazhabobin, bayan haka kuma akwai kalmomin da suka kebanci tarihin musulunci.

424179




captcha