Bangaren kasa da kasa; Babban sakataren kungiyar kula da yada ilimin da al'adun addinin musulunci Abduaziz Altuwaijari ya bayyana muhimmancin da ke tattare da taka rawar jami'oin kasashen musulmi a matsayi na kasa da kasa a dukkanin bangarori na ilimi, ta yadda hakan zai ba su damar bayyana wa duniya irin ci gaban da musulunci yake tattare da shi ta dukkanin fuskoki.