Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani zaman taro kan kur'ani mai tsarki a yankin Katif na kasar saudiyya, wanda ke samun halartar mahardata kur'ani gami da makaranta da kuma masana da malaman mazhabar shi'a na kasar Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga tashar talabijin din kasar Saudiyya ta Walfajr cewa; An fara gudanar da wani zaman taro kan kur'ani mai tsarki a yankin Katif na kasar saudiyya, wanda ke samun halartar mahardata kur'ani gami da makaranta da kuma masana da malaman mazhabar shi'a na kasar Saudiyya. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wannan taro ita ce karfafa gwiwar maharda da makarnta kur'ani mai tsarki na yankin, inda yabnzu sama da daliban makarantun kur'ani sama da 3000 ke halartar taron, daga makarantu 128. daga cikin abubuwan da taron ke mayar da hankali kansu akwai batun shigar al'adun turai da sauran kasashen da ba na musulunci wadanda kan gurbata al'adun matasa.
424243