Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta mata a kasar Katar, wadda za a fara gudanarwa a cikin watan Ramadan mai zuwa a birnin Doha fadar mulkin kasar ta Katar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Al-raya ta kasar Katar cewa; Za a fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta mata a kasar Katar, wadda za a fara gudanarwa a cikin watan Ramadan mai zuwa a birnin Doha fadar mulkin kasar ta Katar. Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyar kula da harkokin kur'ani a kasar Katar ita ce ta shirya gudanar da wannan gasar, inda mahadarta da makaranta mata kimanin 200 na kasar Katar za su halarci wannan gasar. Daga cikin muhimman abubuwan da gasar za ta mayar da hankali kansu akwai bangaren harda da kuma kira'a, za a bayar da kyuatuka na musamman ga wadanda suka lashe gasar.
424944