Bangaren kasa da kasa; An buga tare da yada littafin da ke dauke da manufofin kungiyar yada ilmi da al'adun addinin Musulunci ta ISESCO bayan kwashe shekaru 27 da kafa kungiyar, an kuma fassara littafin a cikin harsunan larabci da kuma turanci gami da faransanci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga majiyoyi masu zaman kansu cewa; An buga tare da yada littafin da ke dauke da manufofin kungiyar yada ilmi da al'adun addinin Musulunci ta ISESCO bayan kwashe shekaru 27 da kafa kungiyar, an kuma fassara littafin a cikin harsunan larabci da kuma turanci gami da faransanci. Bayanin ya ci gaba da cewa; Babban daraktan kungiyar ta ISESCO da ke kula da harkokin ilmi da al'adu na addinin Musulunci da ke karkashin kulawar kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Abdulaziz Tuwaijari ya bayyana cewa; littafin yana dauke da muhimman abubuwa da suka shafi al'adu da kuma ilmomi da ya kamata dukkanin kasashen musulmi su samu masaniya kansu, a kan haka ne ma aka fassara littafin zuwa wasu yaruka manya na duniya.
424874