IQNA

An Gudanar Da Taro Kan Mayar Da Martani Ga Masu Sukar Musulunci Ta Internet

13:48 - June 25, 2009
Lambar Labari: 1794812
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani taro dangane da hanyoyin da ya kamata a bi wajen mayar da martani ga masu sukar addinin Musulunci ta hanyar internet, wanda masana musulmi da kuma injiniyoyi da suka san harkokin yanar gizo suka halarta.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alakhbar ta kasar Masar cewa; An gudanar da wani taro dangane da hanyoyin da ya kamata a bi wajen mayar da martani ga masu sukar addinin Musulunci ta hanyar internet, wanda masana musulmi da kuma injiniyoyi da suka san harkokin yanar gizo suka halarta. Bayanin ya ci gaba da cewa babban makasudin gudanar da wannan taro shi ne, a cikin 'yan lokutannan wasu kasashen yammacin turai da suka hada da Amurk ada kuma Isra'ila a gefe guda sun bude shafukan internet domin bata sunan addinin Musulunci a idon al'ummomin duniya, daga cikin shafukan akwai wasu 20 da Amurka da isra'ila ne suka bude su kuma suke daukar nauyinsu.

424815




captcha