Bangaren kasa da kasa; Kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta yi Allawadai da ziyarar tsokana da minista mai kula da harkokin tsaro na cikin a Haramtacciyar Kasar Isra'ila ya kai a masallacin Qods mai alfarma, tare da yin kira da a kawo karshen hakan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Syria na sana cewa; Sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa Amr Musa ya bayyana cewa; Kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta yi Allawadai da ziyarar tsokana da minista mai kula da harkokin tsaro na cikin a Haramtacciyar Kasar Isra'ila ya kai a masallacin Qods mai alfarma, tare da yin kira da a kawo karshen hakan. Bayanin ya ci gaba da cewa, ziyarar ta minista mai kula da harkokin tsaro na cikin gida a Isra'ila wani salon a tsokanar al'ummar musulmi da larabawa, kuma hakan ba abu ne da za a sa ido ba tare da mayar da martani kansa ba. Amr Musa ya ce ya zama wajibi kan Isra'ila ta kawo karshen ayyukan tsokana da take yi wa al'ummomin musulmi da na larabawa.
424799