Bangaren siyasa da zamantakewa: Hang Sawi Kit shugaban Babban bankin Sangapur ya jaddada maganar kafa madogara daya cilo da za ta sa ido kan bankin musulunci.
Daga kudu maso gabacin Asiya ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar kasa da kasa ta Alshark Al'ausat ta watsa rahoton cewa: Hang Sawi Kit a wata tattaunawa day a yi da wannan jaridar ya bayyana cewa; taro karo na shidda da za a gudanar na majalisar kula da kudade a Sangapur zai fitar da matsayin wannan kasa da rawar da take takawa ta fuskar sha'anin day a shafi banki a musulunci kuma Sangapur na daya daga cikin mambobin majalisar da iya kawo canji da ci gaba a wannan manufa da abin da ake son cimma.
424910