IQNA

An Bude Wata Cibiyar Ilmomi Da Al'adun Musulunci A Jamus

9:00 - June 28, 2009
Lambar Labari: 1795556
Bangaren kasa da kasa; An bude wata cibiyar kla da harkokin al'adu da ilmomin addinin musulunci a jami'ar Berlin da ke kasar Jamus, wanda taron ya samu halartar jamia'ai daga kasashen musulmi daban-daban da suka hada da Iran Malazia da dai sauransu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya cewa; An bude wata cibiyar kla da harkokin al'adu da ilmomin addinin musulunci a jami'ar Berlin da ke kasar Jamus, wanda taron ya samu halartar jamia'ai daga kasashen musulmi daban-daban da suka hada da Iran Malazia da dai sauransu. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar bude wannan cibiya shi ne kara karfafa harkokin yada ilimi da al'adu na addinin musulunci a nahiyar turai, kuma an zabi jamus ne kasantuwarta tana tsakiyar kasashen turai, kuma akwai mabiya adddinin musulunci da dama a cikin kasar.
425598

captcha