IQNA

An Fara Gudanar Da Wani Shirin Bayar Da Horo Ga Limamai A Morocco

8:59 - June 28, 2009
Lambar Labari: 1795561
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani shiri na bayar da hro ga limaman masallatai a kasar Morocco, da nufin kara ilmantar da su kan hukunce-hukuncen musulunci, wanda kuma shirin ya hada d masu kula da harkokin cibiyoyin musulunci na kasar da ma makarantun addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na middle east online cewa; An fara gudanar da wani shiri na bayar da hro ga limaman masallatai a kasar Morocco, da nufin kara ilmantar da su kan hukunce-hukuncen musulunci, wanda kuma shirin ya hada d masu kula da harkokin cibiyoyin musulunci na kasar da ma makarantun addinin musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa minista mai kula da harkokin addinin musulunci na kasar Morcco Ahmad Taufik shi ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa sarkin kasar ne ya sa aka ware wasu kudi tun a shekarar da ta gabata domin aiwatar da wannan shiri, kudin sun kai kimanin yuro miliya goma sha tara.

425584


captcha