IQNA

Wakilan Kasashen Musulmi Sun Gana Da Waziriyar Jamus

8:58 - June 28, 2009
Lambar Labari: 1795566
Bangaren kasa da kasa; Wakilan kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC sun gana da waziriyar kasar Jamus Angela Micheil a birnin Berlin na fadar mulkin kasar jamus, wanda kuma wannan na daya daga cikin tarukan shekare-shekara da suka saba gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na gundhaerber cewa; Wakilan kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC sun gana da waziriyar kasar Jamus Angela Micheil a birnin Berlin na fadar mulkin kasar jamus, wanda kuma wannan na daya daga cikin tarukan shekare-shekara da suka saba gudanarwa. A yayin ganawar ta su sun tabo muhimman batutuwa da suka shafi dangantaka tsakanin kasar jamus da kuma kasashen musulmi, da irin rawar da ya kamata jamus ta taka wajen kyautata dangantaka tsakanin kasashen musulmi da na turai. A bangare guda kuma wanda ya jaoranci tawagar ya jadda irin muhimmancin da ke tattare da rawar da Turkiya ke takawa ta fuskacin karfafa harkkin musulmi a kasar Jamus.

425575


captcha